Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 9:21-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Saul ya ce, “Ni mutumin kabilar Biliyaminu ne, kabilar da ta fi ƙanƙanta a Isra'ila. Iyalina kuma su ne mafi ƙanƙanta a iyalan kabilar Biliyaminu. Me ya sa ka faɗa mini irin wannan magana?”

22. Sa'an nan Sama'ila ya shigar da Saul da baransa a babban ɗakin taruwa, ya sa su zauna gaba inda baƙi suke, wajen mutum talatin aka gayyata.

23. Sama'ila kuwa ya ce wa mai dahuwa, “Kawo naman nan da na ba ka, wanda na ce ka ajiye shi dabam.”

24. Sai mai dahuwa ya kawo cinya da gadon baya ya ajiye a gaban Saul. Sa'an nan Sama'ila ya ce, “Sai ka ci naman da aka ajiye a gabanka, gama dominka aka ajiye shi don ka ci a wannan lokaci tare da waɗanda na gayyata.”A wannan rana kuwa Saul ya ci tare da Sama'ila.

25. Sa'ad da suka gangaro daga wurin yin sujadar zuwa cikin gari, sai aka shirya wa Saul gado a kan bene.

26. Ya kwanta, ya yi barci.Da asuba, Sama'ila ya kira Saul ya ce, “Tashi, in sallame ka.” Saul kuwa ya tashi, shi da Sama'ila suka fita waje zuwa kan titi.

27. Sa'ad da suka kai bayan gari, sai Sama'ila ya ce wa Saul, “Ka sa baranka ya yi gaba, kai ka tsaya nan tukuna domin in faɗa maka abin da Allah ya ce.”

Karanta cikakken babi 1 Sam 9