Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 5:4-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Kashegari da safe kuma da suka tashi, sai suka ga Dagon ya faɗi rubda ciki a gaban akwatin alkawarin Ubangiji. Kan Dagon da hannuwansa a gutsure, suna nan a dokin ƙofa. Gangar jikin ce ta ragu.

5. (Saboda haka firistocin Dagon da waɗanda suke sujada a haikalin Dagon ba su taka dokin ƙafar Dagon a Ashdod ba har wa yau.)

6. Ubangiji kuwa ya hukunta mutanen Ashdod ƙwarai da gaske, ya kuma razanar da su, ya azabtar da su da marurai, su da na kewaye da su.

7. Da mutanen Ashdod suka ga yadda abin yake, sai suka ce, “Kada a bar akwatin alkawarin Allah na Isra'ila tare da mu, gama ya tsananta mana, mu da Dagon, allahnmu.”

8. Sai suka aika, aka kirawo dukan sarakunan Filistiyawa, su biyar, suka ce musu, “Me za mu yi da akwatin alkawarin Allah na Isra'ila?”Suka ce, “Sai a kai shi Gat.” Su kuwa suka kai shi can.

Karanta cikakken babi 1 Sam 5