Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 30:21-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Da Dawuda ya zo wurin mutum ɗari biyu ɗin nan waɗanda suka tafke, suka kāsa binsa, waɗanda aka bar su a rafin Besor, sai suka tafi su taryi Dawuda da mutanensa da suka tafi tare da shi. Sa'ad da Dawuda ya zo kusa da su ya gaishe su.

22. Sai dukan mugaye da marasa kirki daga cikin mutanen da suka tafi tare da Dawuda suka ce, “Tun da yake ba su tafi tare da mu ba, ba za mu ba su kome daga cikin ganimar da muka ƙwato ba, sai dai kowane mutum ya ɗauki matarsa da 'ya'yansa ya tafi.”

23. Amma Dawuda ya ce, “'Yan'uwana, ba za ku yi haka da abin da Ubangiji ya ba mu ba. Ubangiji ya kiyaye mu, ya kuma ba da maharan da suka washe mu a hannunmu.

24. Wa zai goyi bayanku a kan wannan al'amari? Wanda ya tafi wurin yaƙi da wanda ya zauna wurin kaya rabonsu zai zama daidai da juna.”

25. Tun daga wannan rana zuwa gaba, wannan ya zama doka da ka'ida ga Isra'ila.

26. Sa'ad da Dawuda ya komo Ziklag, sai ya aika wa abokansa, dattawan Yahuza, da rabo daga cikin ganimar, ya ce, “Ga kyauta dominku, daga cikin ganimar maƙiyan Ubangiji.”

27. Kyautar domin waɗanda suke a Betel, da Ramot ta Negeb, da Yattir,

28. da Arower, da Sifmot, da Eshtemowa,

29. da Rakal, da garuruwa na Yerameyeliyawa, da garuruwa na Ƙan'aniyawa,

Karanta cikakken babi 1 Sam 30