Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 26:7-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Sai Dawuda da Abishai, suka tafi sansanin Saul da dare. Suka tarar da Saul yana barci cikin sansani da mashinsa a kafe a ƙasa, wajen kansa. Abner kuwa da sauran sojoji suna kwance kewaye da shi.

8. Sa'an nan Abishai ya ce wa Dawuda, “Yau Ubangiji ya ba da maƙiyinka a hannunka, ka bar ni in nashe shi da mashi sau ɗaya kaɗai, in sha zararsa, in haɗa shi da ƙasa!”

9. Amma Dawuda ya ce wa Abishai, “Kada ka hallaka shi, gama wa zai taɓa wanda Ubangiji ya keɓe, ya rasa yin laifi?

10. Hakika Ubangiji zai buge shi, ko ajalinsa ya auka, ko kuwa ya hallaka a wurin yaƙi.

11. Ubangiji ya sawwaƙa in miƙa hannuna in taɓa wanda Ubangiji ya keɓe. Sai dai ka ɗauki mashin da butar ruwan da yake wajen kansa, mu tafi.”

12. Da haka Dawuda ya ɗauki mashi da butar ruwan da yake wajen kan Saul, suka tafi. Ba wanda ya gansu, ba wanda ya sani, ba kuwa wanda ya farka, gama dukansu suna barci, domin Ubangiji ne ya sa barci mai nauyi ya share su.

13. Sa'an nan Dawuda ya haye zuwa wancan gefe, ya tsaya can nesa bisa dutsen, da ɗan nisa tsakaninsu.

14. Sai Dawuda ya kira sojojin sansanin, da kuma Abner ɗan Ner, ya ce, “Ba za ka amsa mini ba, Abner?”Sai Abner ya ce, “Wa yake kiran sarki?”

15. Dawuda ya ce wa Abner, “Kai ba namiji bane? Wa yake kama da kai cikin Isra'ila? Me ya sa ba ka lura da mai girma, sarki ba? Wani mutum ya zo don ya hallaka mai girma sarki.

16. Abin da ka yi ba shi da kyau. Ka isa a kashe ka, da yake ba ka lura da mai girma ba, wanda Ubangiji ya keɓe. Ka duba, ina mashin sarki da butar ruwan da yake wajen kansa suke?”

17. Saul ya gane da muryar Dawuda, ya ce, “Muryarka ke nan ɗana, Dawuda?”Dawuda ya amsa, “I, muryata ce, ya mai girma sarki.”

18. Sai ya ƙara da cewa, “Me ya sa mai girma yake bin sawun baransa? Me na yi? Mene ne laifina?

19. Bari sarki ya kasa kunne ga maganar baransa. Idan Ubangiji ne ya kuta ka ka yi gāba da ni, to, bari ya karɓi hadaya, amma idan mutane ne, to, bari su zama la'anannu, gama sun kore ni don kada in sami rabo cikin gādon Ubangiji, suna cewa, ‘Tafi ka bauta wa alloli.’

20. Kada ka kashe ni a baƙuwar ƙasa nesa da Ubangiji. Don me Sarkin Isra'ila yake so ya kashe ni, ni da nake kamar tunkuyau? Don me zai farauce ni kamar tsuntsun jeji?”

Karanta cikakken babi 1 Sam 26