Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Dawuda Ya Bar Saul da Rai a Zif

1. Zifawa suka zo wurin Saul a Gibeya suka ce, “Ba ga Dawuda yana ɓuya a kan tudun Hakila wanda yake gaban Yeshimon ba?”

2. Saul kuwa ya tashi ya tafi jejin Zif tare da zaɓaɓɓu dubu uku (3,000) na Isra'ila don ya nemi Dawuda.

3. Ya kafa sansaninsa a kan tudun Hakila wanda yake gefen hanya, a gaban Yeshimon. Amma Dawuda ya yi zamansa a jeji. Da ya ga Saul ya bi shi cikin jejin,

4. sai ya aiki magewaya, suka tabbata lalle Saul ya zo.

5. Dawuda kuwa ya tashi ya tafi wurin da Saul ya kafa sansani. Ya kuwa ga inda Saul yake kwance, da kuma Abner ɗan Ner, sarkin yaƙin Saul. Saul ya kwanta a sansanin, sojojin suna kewaye da shi.

6. Dawuda ya ce wa Ahimelek Bahitte, da Abishai, ɗan Zeruya, ɗan'uwan Yowab, “Wa zai tafi tare da ni zuwa sansanin Saul?”Abishai ya ce, “Zan tafi tare da kai.”

7. Sai Dawuda da Abishai, suka tafi sansanin Saul da dare. Suka tarar da Saul yana barci cikin sansani da mashinsa a kafe a ƙasa, wajen kansa. Abner kuwa da sauran sojoji suna kwance kewaye da shi.

8. Sa'an nan Abishai ya ce wa Dawuda, “Yau Ubangiji ya ba da maƙiyinka a hannunka, ka bar ni in nashe shi da mashi sau ɗaya kaɗai, in sha zararsa, in haɗa shi da ƙasa!”

9. Amma Dawuda ya ce wa Abishai, “Kada ka hallaka shi, gama wa zai taɓa wanda Ubangiji ya keɓe, ya rasa yin laifi?

10. Hakika Ubangiji zai buge shi, ko ajalinsa ya auka, ko kuwa ya hallaka a wurin yaƙi.

11. Ubangiji ya sawwaƙa in miƙa hannuna in taɓa wanda Ubangiji ya keɓe. Sai dai ka ɗauki mashin da butar ruwan da yake wajen kansa, mu tafi.”

12. Da haka Dawuda ya ɗauki mashi da butar ruwan da yake wajen kan Saul, suka tafi. Ba wanda ya gansu, ba wanda ya sani, ba kuwa wanda ya farka, gama dukansu suna barci, domin Ubangiji ne ya sa barci mai nauyi ya share su.

13. Sa'an nan Dawuda ya haye zuwa wancan gefe, ya tsaya can nesa bisa dutsen, da ɗan nisa tsakaninsu.

14. Sai Dawuda ya kira sojojin sansanin, da kuma Abner ɗan Ner, ya ce, “Ba za ka amsa mini ba, Abner?”Sai Abner ya ce, “Wa yake kiran sarki?”

15. Dawuda ya ce wa Abner, “Kai ba namiji bane? Wa yake kama da kai cikin Isra'ila? Me ya sa ba ka lura da mai girma, sarki ba? Wani mutum ya zo don ya hallaka mai girma sarki.

16. Abin da ka yi ba shi da kyau. Ka isa a kashe ka, da yake ba ka lura da mai girma ba, wanda Ubangiji ya keɓe. Ka duba, ina mashin sarki da butar ruwan da yake wajen kansa suke?”

17. Saul ya gane da muryar Dawuda, ya ce, “Muryarka ke nan ɗana, Dawuda?”Dawuda ya amsa, “I, muryata ce, ya mai girma sarki.”

18. Sai ya ƙara da cewa, “Me ya sa mai girma yake bin sawun baransa? Me na yi? Mene ne laifina?

19. Bari sarki ya kasa kunne ga maganar baransa. Idan Ubangiji ne ya kuta ka ka yi gāba da ni, to, bari ya karɓi hadaya, amma idan mutane ne, to, bari su zama la'anannu, gama sun kore ni don kada in sami rabo cikin gādon Ubangiji, suna cewa, ‘Tafi ka bauta wa alloli.’

20. Kada ka kashe ni a baƙuwar ƙasa nesa da Ubangiji. Don me Sarkin Isra'ila yake so ya kashe ni, ni da nake kamar tunkuyau? Don me zai farauce ni kamar tsuntsun jeji?”

21. Sa'an nan Saul ya ce, “Na yi laifi, ka komo, ɗana Dawuda, ba zan yi maka kome ba, gama raina ya zama da daraja a gare ka kyau. Na yi aikin wauta, na yi laifi da yawa.”

22. Sai Dawuda ya ce, “Ga mashinka! Ka aiko wani saurayi ya zo ya karɓa.

23. Ubangiji dai zai sāka wa kowa bisa ga adalcinsa da amincinsa. Ubangiji ya bashe ka a hannuna yau, amma na ƙi in kashe wanda Ubangiji ya keɓe.

24. Kamar yadda ranka ya zama da daraja a gare ni yau, bari raina kuma ya zama da daraja a gaban Ubangiji, ya cece ni daga dukan wahala.”

25. Sai Saul ya ce wa Dawuda, “Ubangiji ya sa maka albarka, ɗana Dawuda, za ka yi manyan abubuwa, ka kuwa yi nasara!”Dawuda dai ya yi tafiyarsa, Saul kuma ya koma gidansa.