Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 26:3-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Ya kafa sansaninsa a kan tudun Hakila wanda yake gefen hanya, a gaban Yeshimon. Amma Dawuda ya yi zamansa a jeji. Da ya ga Saul ya bi shi cikin jejin,

4. sai ya aiki magewaya, suka tabbata lalle Saul ya zo.

5. Dawuda kuwa ya tashi ya tafi wurin da Saul ya kafa sansani. Ya kuwa ga inda Saul yake kwance, da kuma Abner ɗan Ner, sarkin yaƙin Saul. Saul ya kwanta a sansanin, sojojin suna kewaye da shi.

6. Dawuda ya ce wa Ahimelek Bahitte, da Abishai, ɗan Zeruya, ɗan'uwan Yowab, “Wa zai tafi tare da ni zuwa sansanin Saul?”Abishai ya ce, “Zan tafi tare da kai.”

7. Sai Dawuda da Abishai, suka tafi sansanin Saul da dare. Suka tarar da Saul yana barci cikin sansani da mashinsa a kafe a ƙasa, wajen kansa. Abner kuwa da sauran sojoji suna kwance kewaye da shi.

8. Sa'an nan Abishai ya ce wa Dawuda, “Yau Ubangiji ya ba da maƙiyinka a hannunka, ka bar ni in nashe shi da mashi sau ɗaya kaɗai, in sha zararsa, in haɗa shi da ƙasa!”

9. Amma Dawuda ya ce wa Abishai, “Kada ka hallaka shi, gama wa zai taɓa wanda Ubangiji ya keɓe, ya rasa yin laifi?

10. Hakika Ubangiji zai buge shi, ko ajalinsa ya auka, ko kuwa ya hallaka a wurin yaƙi.

11. Ubangiji ya sawwaƙa in miƙa hannuna in taɓa wanda Ubangiji ya keɓe. Sai dai ka ɗauki mashin da butar ruwan da yake wajen kansa, mu tafi.”

Karanta cikakken babi 1 Sam 26