Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 25:35-44 Littafi Mai Tsarki (HAU)

35. Sai Dawuda ya karɓi abin da ta kawo masa. Ya ce mata, “Ki koma gida kada ki damu. Zan yi abin da kike bukata.”

36. Abigail ta koma wurin Nabal, ta iske shi yana biki irin na sarakuna a gidansa. Ya yi ta nishaɗi, ya bugu sosai, don haka ba ta ce masa kome ba sai da safe.

37. Da safe, sa'ad da ruwan inabi ya sake shi, sai Abigail ta faɗa masa abin da ya faru. Zuciyarsa kuwa ta tsinke gaba ɗaya.

38. Bayan kwana goma sai Ubangiji ya bugi Nabal, ya mutu.

39. Sa'ad da Dawuda ya ji Nabal ya mutu, sai ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji wanda ya sāka mini a kan irin rainin da Nabal ya yi mini. Ya kuma hana ni aikata mugunta. Ya ɗora wa Nabal muguntarsa a kansa.”Sa'an nan Dawuda ya aika, ya nemi Abigail ta zama matarsa.

40. Da barorin Dawuda suka zo wurin Abigail a Karmel, suka ce mata, “Dawuda ne ya aiko mu wurinki domin mu kai ki wurinsa, ki zama matarsa.”

41. Sai ta rusuna har ƙasa, ta ce, “Ni baranyarsa ce, ina a shirye in wanke ƙafafun barorinsa.”

42. Sai ta yi hanzari ta hau jaki, ta ɗauki kuyanginta, su biyar, ta tafi tare da manzannin Dawuda, ta zama matarsa.

43. Dawuda kuma ya auro Ahinowam Bayezreyeliya, dukansu biyu kuwa suka zama matansa.

44. Amma Saul ya aurar da Mikal, 'yarsa, matar Dawuda, ga Falti ɗan Layish wanda yake a Gallim.

Karanta cikakken babi 1 Sam 25