Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 25:13-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Sai Dawuda ya ce wa mutanensa, “Kowa ya rataya takobinsa.” Ko wannensu kuwa ya rataya takobi. Dawuda kuma ya rataya nasa takobi. Mutum wajen arbaminya suka tafi tare da shi. Mutum metan kuwa suka zauna a wurin kayayyakinsu.

14. Sai ɗaya daga cikin samarin Nabal ya faɗa wa Abigail, wato matar Nabal cewa, “Dawuda ya aiko manzanninsa daga jeji su gai da maigida, amma maigida ya zazzage su.

15. Ga shi, mutanen kuwa sun yi mana kirki, ba mu sha wata wahala ba, ba abin da ya ɓace mana dukan lokacin da muke tare da su a jeji.

16. Sun zama mana ganuwa dare da rana dukan lokacin da muke tare da su a wurin kiwon tumaki.

17. Yanzu sai ki yi tunani, ki san abin da ya kamata ki yi, gama ana niyyar yi wa maigida da dukan gidansa ɓarna. Ga shi, maigida yana da mugun hali, ba zai ji kowa ba!”

18. Sai Abigail ta yi sauri, ta ɗauki malmalar abinci guda metan, da salkar ruwan inabi biyu, da tumaki biyar da aka gyara, da soyayyen hatsi mudu uku, da nonnan 'ya'yan inabi guda ɗari, da kauɗar ɓaure guda metan, ta labta wa jakai.

19. Ta ce wa samarin, “Ku yi gaba, ga ni nan tafe bayanku.” Amma ba ta faɗa wa Nabal, mijinta ba.

20. Tana tafiya a kan jaki, ta kai gindin wani dutse ke nan, sai ga Dawuda da mutanensa tafe. Ta tafi, ta sadu da su.

21. Dawuda ya ce a ransa, “Ashe, a banza ne na yi ta lura da dukan abin da yake na mutumin nan a jeji, har ba abin da yake nasa da ya ɓace. Ga shi, ya rama mini alheri da mugunta.

22. Allah ya buge ni in mutu, idan na bar masa wani mutum da rai kafin gobe da safe.”

23. Da Abigail ta ga Dawuda, sai ta yi sauri ta sauka daga kan jakin, ta durƙusa gabansa har ƙasa.

24. Ta faɗi a ƙafafunsa, ta ce, “Ya shugabana, bari laifin ya zama nawa. Ina roƙonka ka bar baiwarka ta yi magana, ka kuma yarda ka ji maganar baiwarka.

25. Kada maigidana ya kula da Nabal, gama wawa ne, kamar yadda sunansa yake, wato wawa. Ni dai ban ga samarin da ubangijina ya aika ba.

Karanta cikakken babi 1 Sam 25