Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 23:14-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Dawuda ya zauna a ɓoye cikin jeji a ƙasar tudu ta jejin Zif. Saul kuwa ya yi ta nemansa kowace rana, amma Ubangiji bai ba da Dawuda a hannunsa ba.

15-16. Dawuda kuwa ya ji tsoro, gama Saul ya fito don ya farauci ransa.Sa'ad da yake cikin jejin Zif, a Horesh, sai Jonatan ɗan Saul, ya zo wurinsa, ya tabbatar masa da kiyayyewar Allah.

17. Ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, gama Saul, mahaifina ba zai same ka ba. Za ka zama Sarkin Isra'ila, ni kuma zan zama wazirinka. Saul mahaifina ya san da haka.”

18. Su biyu fa suka yi wa juna alkawari a gaban Ubangiji. Dawuda ya zauna a Horesh, Jonatan kuwa ya koma gida.

19. Sai Zifawa suka haura zuwa wurin Saul a Gibeya, suka ce masa, “Dawuda ya ɓuya a ƙasarmu cikin Horesh a kan tudun Hakila da yake kudu da jejin Yahuza.

20. Sai ka gangara, ka zo, ya sarki, ta yadda kake so. Mu za mu bashe shi a hannun sarki.”

21. Saul ya ce, “Ubangiji ya sa muku albarka, gama kuna jin juyayina.

22. Ku tafi, ku ƙara tabbatar da inda ya ɓuya, da wanda ya gan shi a wurin, gama an faɗa mini, cewa shi mai wayo ne.

23. Ku lura sosai da dukan wuraren da yake ɓuya, sa'an nan ku komo mini da tabbataccen labari. Sa'an nan zan tafi tare da ku. Idan yana ƙasar, zan neme shi ko'ina a ƙasar Yahuza.”

24. Sai suka yi gaba, suka tafi Zif. Dawuda da mutanensa kuwa suna jejin Mawon, cikin Araba, kudu da Yeshimon.

25. Saul da mutanensa suka tafi neman Dawuda. Da Dawuda ya ji labari, sai ya sauka daga dutsen ya zauna a can jejin Mawon. Da Saul ya ji, sai ya bi Dawuda zuwa jejin Mawon.

26. Saul yana gefe ɗaya na dutsen, Dawuda kuma da mutanensa suna wancan gefe. Dawuda ya yi sauri ya tsere daga Saul domin Saul da mutanensa suna ƙoƙari su kewaye su, su kama su.

27. Suna bin su Dawuda kusa kusa, sai manzo ya zo ya ce wa Saul, “Sai ka komo da sauri domin Filistiyawa sun kawo wa ƙasar hari.”

28. Saul kuwa ya koma daga bin Dawuda, ya tafi, ya yi yaƙi da Filistiyawa, domin haka aka riƙa kiran wurin, Sela-hammalekot, wato dutsen tserewa.

29. Dawuda kuwa ya tashi daga can, ya tafi jejin En-gedi inda ya ɓuya.

Karanta cikakken babi 1 Sam 23