Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 23:11-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Ko mutanen Kaila za su bashe ni a hannunsa? Ko Saul zai zo kamar yadda na ji? Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, ina roƙonka ka faɗa wa bawanka.”Ubangiji kuwa ya ce, “Saul zai zo.”

12. Dawuda kuma ya ce, “Mutanen Kaila za su bashe ni da mutanena a hannun Saul?”Ubangiji ya ce masa, “Za su bashe ku.”

13. Sa'an nan Dawuda da mutanen da suke tare da shi, mutum wajen ɗari shida, suka tashi daga Kaila, suka tafi inda hali ya kai su. Da Saul ya ji Dawuda ya tsere daga Kaila, sai ya fasa tafiya can.

14. Dawuda ya zauna a ɓoye cikin jeji a ƙasar tudu ta jejin Zif. Saul kuwa ya yi ta nemansa kowace rana, amma Ubangiji bai ba da Dawuda a hannunsa ba.

15-16. Dawuda kuwa ya ji tsoro, gama Saul ya fito don ya farauci ransa.Sa'ad da yake cikin jejin Zif, a Horesh, sai Jonatan ɗan Saul, ya zo wurinsa, ya tabbatar masa da kiyayyewar Allah.

17. Ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, gama Saul, mahaifina ba zai same ka ba. Za ka zama Sarkin Isra'ila, ni kuma zan zama wazirinka. Saul mahaifina ya san da haka.”

18. Su biyu fa suka yi wa juna alkawari a gaban Ubangiji. Dawuda ya zauna a Horesh, Jonatan kuwa ya koma gida.

19. Sai Zifawa suka haura zuwa wurin Saul a Gibeya, suka ce masa, “Dawuda ya ɓuya a ƙasarmu cikin Horesh a kan tudun Hakila da yake kudu da jejin Yahuza.

Karanta cikakken babi 1 Sam 23