Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 22:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Dawuda ya bar Gat, ya tsere zuwa kogon Adullam. Da 'yan'uwansa da mutanen gidan ubansa, suka ji labari, suka tafi can wurinsa.

2. Kowane mutum kuma da yake matse, da wanda ake bi bashi, da wanda ransa ba ya kwance, suka tattaru a wurin Dawuda. Shi kuwa ya zama shugabansu. Sun kai wajen mutum ɗari huɗu.

3. Daga can Dawuda ya wuce zuwa Mizfa ta Mowab. Ya ce wa Sarkin Mowab, “Ina roƙonka, ka yarda mahaifina da mahaifiyata su zo su zauna a wurinka kafin in san abin da Ubangiji zai yi da ni.”

4. Sai ya bar iyayensa a wurin Sarkin Mowab, suka zauna a wurinsa duk lokacin da Dawuda yake ta ɓuya a kogwannin duwatsu.

5. Sa'an nan Gad, annabi, ya ce wa Dawuda, “Kada ka zauna a nan, maza ka tafi ƙasar Yahuza.” Sai ya tashi, ya tafi kurmin Haret.

6. Sai Saul ya ji labari an gane inda Dawuda da mutanensa suke. Saul kuwa yana zaune a Gibeya a gindin itacen tsamiya a kan tudu, yana riƙe da mashinsa. Dukan fādawansa suna tsaye kewaye da shi.

7-8. Sai ya ce wa fādawan da suke tsaye kewaye da shi, “Ku ji, ya ku mutanen Biliyaminu, ɗan Yesse zai ba kowannenku gonaki, da gonakin inabi ne? Zai maishe ku shugabanni na dubu dubu, da na ɗari ɗari, har da dukanku kuka yi mini maƙarƙashiya? Ba wanda ya sanar da ni sa'ad da ɗana ya haɗa kai da ɗan Yesse? Ba wanda ya damu saboda da ni, balle a faɗa mini yadda ɗana ya kuta barana ya tayar mini, yana fakona, kamar yadda yake a yau?”

9. Sa'an nan Doyeg, mutumin Edom, da yake tsaye tare da fādawan Saul, ya ce, “Na ga ɗan Yesse yana zuwa Nob wurin Ahimelek, ɗan Ahitub.

10. Shi kuwa ya roƙi Ubangiji domin Dawuda, ya kuma ba shi guzuri, har ya ba shi takobin Goliyat, Bafilisten.”

11. Sarki kuwa ya aika a kira Ahimelek, firist, ɗan Ahitub, da dukan mutanen gidan mahaifinsa, da firistocin da suke a Nob. Dukansu kuwa suka zo wurin sarki.

12. Saul kuwa ya ce, “Ka ji, ya ɗan Ahitub.”Shi kuwa ya amsa ya ce, “Ranka ya daɗe, ina ji.”

13. Saul ya ce masa, “Me ya sa ka yi mini maƙarƙashiya, kai da ɗan Yesse, da yake ka ba shi abinci, da takobi, ka kuma roƙar masa Allah, ga shi yanzu, ya tayar mini, yana fakona, kamar yadda yake yi a yau?”

Karanta cikakken babi 1 Sam 22