Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 21:9-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Firist ya ce, “Ga takobin Goliyat, Bafiliste wanda ka kashe a kwarin Ila, a naɗe da zane a bayan falmaran. Idan kana so ka ɗauka, sai ka ɗauka, gama banda shi, ba wani takobi a nan.”Dawuda kuwa ya ce, “Ai, ba wanda ya fi wannan, sai ka ba ni shi.”

10. Sai Dawuda ya tashi, yana gudu ke nan daga wurin Saul. Ya tafi wurin Akish, Sarkin Gat.

11. Fādawan Akish kuwa suka ce masa, “Ashe, wannan ba shi ne Dawuda, sarkin ƙasar ba? Ba a kansa suka raira waƙa cikin raye-rayensu suna cewa, ‘Saul ya kashe dubbai, Dawuda kuwa ya kashe dubun dubbai’?”

12. Da Dawuda ya ji waɗannan maganganu, sai ya tsorata ƙwarai da Akish Sarkin Gat.

13. Ya mai da kansa kamar mahaukaci a gabansa. Ya yi zane-zane a ƙyamaren ƙofofin garin. Ya bar yau na bin gemunsa.

14. Akish kuwa ya ce wa fādawansa, “Ashe, mutumin mahaukaci ne? Don me kuka kawo shi wurina?

15. Na rasa mahaukata ne da za ku kawo mini wannan mutum ya yi ta hauka a gabana? Wannan mutum ne zai shiga gidana?”

Karanta cikakken babi 1 Sam 21