Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 2:30-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na yi alkawari a dā cewa, ‘Kai da iyalinka da danginka za ku yi mini aikin firist har abada.’ Amma yanzu na ce ba zan yarda da wannan ba. Waɗanda suke girmama ni, zan girmama su. Waɗanda suke raina ni zan ƙasƙantar da su ƙwarai.

31. Ga shi, lokaci yana zuwa da zan karkashe samari cikin iyalinka da danginka, har da ba za a sami wanda zai rayu har ya tsufa a gidanka ba.

32. Za ka kasance da damuwa da jin kishi, za ka duba dukan albarkun da zan sa wa Isra'ila, amma a gidanka ba za a taɓa samun wanda zai rayu har ya tsufa ba.

33. Zan dai bar ɗaya daga zuriyarka da rai, zai yi mini aikin firist, amma zai makance ya fid da zuciya ga kome. Dukan sauran zuriyarka kuwa za su yi mutuwa ƙarfi da yaji.

34. Lokacin da 'ya'yanka biyu, Hofni da Finehas, za su mutu rana ɗaya wannan zai nuna maka abin da na faɗa sai ya cika.

35. Zan zaɓar wa kaina amintaccen firist wanda zai aikata abin da nake so ya yi, zan kuwa ba shi zuriya da ko yaushe za su yi aiki a gaban zaɓaɓɓen sarkina.

36. Dukan wanda ya ragu daga zuriyarka zai je wurin sarki ya roƙi kuɗi da abinci, zai kuma roƙa a yardar masa ya taimaki firistoci da aiki domin ya sami abin da zai ci.”

Karanta cikakken babi 1 Sam 2