Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 2:22-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. Eli kuwa ya tsufa ƙwarai, yana kuma jin dukan abin da 'ya'yansa maza suke yi wa Isra'ilawa, da yadda suke kwana da matan da suke aiki a ƙofar alfarwa ta sujada.

23. Sai ya ce musu, “Me ya sa kuke irin waɗannan abubuwa? Gama kowa yana faɗa mini irin mugayen abubuwan da kuke aikatawa.

24. Haba 'ya'yana, ku bari! Jama'ar Ubangiji suna ta magana a kan wannan mugun abu.

25. Idan mutum ya yi wa wani laifi, Allah yakan kāre shi, amma idan mutum ya yi wa Ubangiji zunubi, wa zai kāre shi?”Amma ba su ji maganar mahaifinsu ba, gama Ubangiji ya riga ya yi shirin kashe su.

26. Yaron nan Sama'ila ya yi ta girma da samun tagomashi a gaban Ubangiji da kuma mutane.

27. Wani annabi ya zo wurin Eli da saƙo daga wurin Ubangiji ya ce, “Sa'ad da kakanka Haruna da iyalinsa suke bauta wa Fir'auna a Masar, na bayyana kaina gare shi.

28. Na zaɓi iyalinsa daga dukan kabilan Isra'ila domin su zama firistocina, su riƙa aiki a bagade, suna ƙona turare, su riƙa ɗaukar keɓaɓɓen akwatina cikin yi mini aiki. Na kuma yardar musu su sami rabonsu daga hadayun da aka ƙona a kan bagade.

29. Me ya sa kuke haɗama a kan hadayuna da sadakokin da na umarta? Eli, don me kake girmama 'ya'yanka fiye da ni, ka bar su suna ta cinye rabo mafi kyau na hadayun jama'ata Isra'ila?

30. Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na yi alkawari a dā cewa, ‘Kai da iyalinka da danginka za ku yi mini aikin firist har abada.’ Amma yanzu na ce ba zan yarda da wannan ba. Waɗanda suke girmama ni, zan girmama su. Waɗanda suke raina ni zan ƙasƙantar da su ƙwarai.

Karanta cikakken babi 1 Sam 2