Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 18:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da Dawuda ya gama magana da Saul, sai zuciyar Jonatan ta saje da ran Dawuda. Jonatan kuwa ya ƙaunaci Dawuda kamar kansa.

2. Daga ran nan Saul ya riƙe Dawuda, bai bari Dawuda ya koma gidan mahaifinsa ba.

3. Jonatan kuma ya yi dawwamammen alkawari da Dawuda, domin shi, wato Jonatan, yana ƙaunar Dawuda kamar kansa.

4. Sai ya tuɓe rigarsa ya ba Dawuda, ya kuma ba shi jabbarsa, da takobinsa, da bakansa, da abin ɗamararsa.

5. Duk inda Saul ya aiki Dawuda, sai ya tafi, ya kuma ci nasara. Saboda haka Saul ya maishe shi shugaban sojoji. Dukan jama'a da barorin Saul kuma suka ji daɗi.

6. Sa'ad da sojoji suke komowa gida, bayan da Dawuda ya komo daga kisan Goliyat, sai mata daga kowane gari na Isra'ila suka fito domin su taryi sarki Saul. Suna raira waƙar farin ciki, suna rawa, suna kaɗa kuwaru da molaye.

7. Suka raira waƙa, suna cewa, “Saul ya kashe dubbai, amma Dawuda ya kashe dubun dubbai.”

Karanta cikakken babi 1 Sam 18