Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 17:39-49 Littafi Mai Tsarki (HAU)

39. Da Dawuda ya sa kayan yaƙin, ya rataya takobi, ya fara tafiya, sai ya ji ba zai iya ba, domin bai saba da su ba. Sai ya ce wa Saul, “Ba zan iya tafiya da waɗannan ba, gama ban saba da su ba.” Ya kuwa tuɓe su.

40. Sa'an nan ya ɗauki sandansa, ya zaɓi duwatsu guda biyar masu sulɓi daga cikin rafi, ya zuba a angararsa. Ya kuma riƙe majajjawarsa, ya tafi, ya fuskanci Bafilisten.

41. Bafilisten kuma ya nufo Dawuda, mai ɗaukar masa garkuwa yana gabansa.

42. Sa'ad da ya ga Dawuda, sai ya raine shi, gama Dawuda saurayi ne kawai, kyakkyawa.

43. Ya ce wa Dawuda, “Ni kare ne da za ka nufo da sanduna?” Ya zagi Dawuda da sunan allolinsu na Filistiyawa.

44. Ya kuma ce wa Dawuda, “Ya ka nan, ni kuwa in ba da namanka ga tsuntsayen sama da namomin jeji.”

45. Dawuda kuwa ya ce masa, “Kai, kana nufo ni da takobi, da mashi, da kēre, amma ni ina zuwa wurinka da sunan Ubangiji Mai Runduna, Allah na sojojin Isra'ila, wanda ka raina.

46. A yau Ubangiji zai bashe ka a hannuna, zan buge ka har ƙasa, in datse kanka, in ba da gawawwakin rundunar Filistiyawa ga tsuntsayen sama da namomin jeji, da haka duniya za ta sani lalle akwai Allah cikin Isra'ila.

47. Taron jama'ar nan kuma za su sani Ubangiji yakan yi ceto ba da takobi da mashi ba, gama yaƙi na Ubangiji ne, zai bashe ku a hannunmu.”

48. Goliyat kuwa ya fara gusowa ya gamu da Dawuda, sai Dawuda ya sheƙa zuwa bakin dāgar yaƙin don ya gamu da shi.

49. Sa'an nan Dawuda ya ɗauko dutse daga cikin angararsa, ya wurga, dutsen kuwa ya sami Goliyat a goshi, har ya lume. Goliyat kuwa ya faɗi rubda ciki.

Karanta cikakken babi 1 Sam 17