Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 17:13-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Manyan 'ya'yansa maza uku sun tafi yaƙi tare da Saul. Sunan babban ɗan, Eliyab, na biye da shi kuma, Abinadab, na ukun kuwa Shimeya.

14. Dawuda shi ne auta. Sa'ad da manyan 'yan'uwansa uku suka tafi tare da Saul wurin yaƙi,

15. Dawuda yakan koma Baitalami lokaci lokaci domin kiwon tumakin mahaifinsa.

16. Goliyat yana ta tsokanar Isra'ilawa safe da maraice, har kwana arba'in.

17. Wata rana ke nan, sai Yesse ya ce wa Dawuda, ɗansa, “Ka ɗauki wannan tumammen hatsi, da malmalar abinci goma, ka kai wa 'yan'uwanka da sauri a sansanin.

18. Ga waɗannan dunƙulen cuku goma, ka kai wa shugaba na mutum dubu. Ka dubo lafiyar 'yan'uwanka, ka kawo mini labari.

19. Da Saul, da 'yan'uwanka, da dukan mazajen Isra'ila suna kwarin Ila, suna yaƙi da Filistiyawa.”

20. Kashegari sai Dawuda ya tashi tun da sassafe, ya bar tumaki a hannun wani makiyayi, ya ɗauki guzurin, ya tafi kamar yadda mahaifinsa, Yesse, ya umarce shi. Ya isa sansani daidai lokacin da runduna suke fita tana kirari na jān dāgar yaƙi.

21. Isra'ilawa da Filistiyawa suka jā dāga, runduna gāba da runduna.

22. Sai Dawuda ya bar abin da ya kawo a wurin mai jiran kaya, ya sheƙa zuwa bakin dāga domin ya gai da 'yan'uwansa.

23. Sa'ad da yake magana da su, sai ga Goliyat, jarumin Filistiyawa na Gat, ya fito daga rundunar Filistiyawa, ya yi maganganu irin na dā. Dawuda kuwa ya ji.

24. Sa'ad da dukan mazajen Isra'ila suka ga mutumin, suka guje masa saboda tsoro.

Karanta cikakken babi 1 Sam 17