Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 17:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai Filistiyawa suka tattaru a Soko ta Yahuza, suka kafa sansani a tsakanin Soko da Azeka, a Efes-dammim.

2. Saul kuma da mutanen Isra'ila suka tattaru, suka kafa sansani a kwarin Ila, suka jā dāga don su yi yaƙi da Filistiyawa.

3. Filistiyawa suka jeru a tudu guda, Isra'ilawa kuwa a ɗaya tudun. Kwari yana tsakaninsu.

4. Akwai wani jarumi, sunansa Goliyat, ya fito daga sansanin Filistiyawa. Tsayinsa kamu shida da rabi.

5. Yana sa kwalkwali na tagulla a kansa, yana kuma saye da sulke na tagulla wanda nauyinsa ya fi shekel dubu biyar (5,000).

6. Ya sa safa ta tagulla a ƙafafunsa, yana kuma da mashi na tagulla saɓe a kafaɗarsa.

7. Gorar mashinsa ta yi kama da dirkar masaƙa. Nauyin ruwan mashinsa na baƙin ƙarfe shekel ɗari shida ne. Mai ɗaukar masa garkuwa yana tafe a gabansa.

Karanta cikakken babi 1 Sam 17