Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 14:37-47 Littafi Mai Tsarki (HAU)

37. Saul kuwa ya yi tambaya ga Ubangiji, ya ce, “In runtumi Filistiyawa? Za ka bashe su ga Isra'ilawa?” Amma Ubangiji bai amsa masa a wannan rana ba.

38. Sai Saul ya ce wa shugabanni, “Ku zo nan dukanku don mu bincike, mu san zunubin da aka yi a yau.

39. Hakika, duk wanda ya yi laifin za a kashe shi, ko da Jonatan ne, ɗana.” Amma ba wanda ya ce kome.

40. Ya kuma ce, “Dukanku ku tsaya waje ɗaya, ni kuma da Jonatan, ɗana, mu tsaya waje ɗaya.”Sai jama'ar suka ce wa Saul, “Ka yi abin da ya yi maka kyau.”

41. Sa'an nan Saul ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, me ya sa ba ka amsa mini ba a wannan rana? Idan wannan laifina ne, ko kuwa na ɗana, Jonatan, ya Ubangiji Allah na Isra'ila, ka nuna mana.” Sai amsa ta nuna Jonatan da Saul ne, jama'a kuwa suka kuɓuta.

42. Sa'an nan Saul ya ce, “A jefa kuri'a tsakanina da ɗana Jonatan.” Kuri'a kuwa ta fāɗa a kan Jonatan.

43. Sa'an nan Saul ya ce wa Jonatan, “Ka faɗa mini abin da ka yi!” Jonatan ya ce masa, “Na ɗanɗana 'yar zuma ne da na lakata da kan sandan da yake hannuna, ga ni, a shirye nake in mutu.”

44. Sai Saul ya ce, “Allah ya yi mini abin da ya fi haka, idan ba a kashe ka ba, Jonatan.”

45. Amma jama'a suka ce wa Saul, “Jonatan da ya yiwo babbar nasara domin Isra'ila, a ce za a kashe shi? Kai, a'a! Mun yi alkawari ga Ubangiji mai rai, Jonatan ba zai yi hasarar ko gashi guda daga kansa ba. Abin da ya yi a yau, da taimakon Allah ne ya yi.” Da haka mutane suka ceci Jonatan, har ba a kashe shi ba.

46. Sa'an nan Saul ya komo daga runtumar Filistiyawa, suka koma yankin ƙasarsu.

47. Sa'ad da Saul ya ci sarautar Isra'ila, ya yi yaƙi da dukan abokan gābansa da suke kewaye da shi. Ya yi yaƙi da Mowabawa da Ammonawa, da Edomawa, da sarakunan Zoba, da Filistiyawa. Duk inda ya yi yaƙi ya sami nasara.

Karanta cikakken babi 1 Sam 14