Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 14:12-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Sai suka kira Jonatan da mai ɗaukar makamansa, suka ce, “Ku hauro zuwa wurinmu, mu faɗa muku wani abu.”Jonatan kuwa ya ce wa mai ɗaukar makamansa, “Ka biyo ni, gama Ubangiji ya bashe su a hannun Isra'ilawa.”

13. Sa'an nan Jonatan ya hau dutsen da rarrafe, mai ɗaukar makamansa kuwa yana biye da shi. Jonatan ya fāɗa wa Filistiyawa, ya yi ta kā da su, mai ɗaukar makamansa kuma ya bi bayansa yana ta karkashe su.

14. A wannan karo na farko Jonatan da mai ɗaukar makamansa suka kashe mutum wajen ashirin a wani fili mai fāɗi kamar rabin kadada.

15. Dukan Filistiyawan da suke a filin suka ji tsoro, da mahara da sauran sojoji suka yi rawar jiki, ƙasa ta girgiza, aka yi babbar gigicewa.

16. Da matsara na Saul a Gibeya ta Biliyaminu suka duba, sai ga taron Filistiyawa ya watse, kowa ya nufi wajensa, suna tafiya barkatai.

17. Saul ya ce wa mutanen da suke tare da shi, “Ƙidaya mutane yanzu don ku ga wanda ya fita daga cikinmu.” Da aka ƙirga mutanen sai aka tarar Jonatan da mai ɗaukar makamansa ba su nan.

18. Sai Saul ya ce wa Ahaija, “Kawo akwatin alkawarin Allah a nan.” Gama a wannan lokaci akwatin Allah yana hannun Isra'ilawa.

19. Sa'ad da Saul yake magana da firist ɗin, sai hargowa a sansanin Filistiyawa ta yi ta ƙaruwa, Saul kuwa ya ce wa firist, “Janye hannunka.”

20. Sa'an nan Saul da mutanen da suke tare da shi suka taru, suka tafi su yi yaƙi. Sai suka tarar Filistiyawa sun ruɗe suna ta yaƙi da junansu. Aka yi babbar yamutsewa.

21. Ibraniyawan da suke tare da Filistiyawa a dā, waɗanda suka bi su zuwa sansani, suka koma wajen Isra'ilawan da suke tare da Saul da Jonatan.

22. Waɗanda kuma suka bi ta ƙasar tudu ta Ifraimu, da suka ji labari Filistiyawa suna gudu, suka fito suka fafare su.

Karanta cikakken babi 1 Sam 14