Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 13:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Saul yana da shekara talatin sa'ad da ya ci sarauta, ya yi shekara arba'in da biyu yana sarautar Isra'ila.

2. Saul ya zaɓi mutum dubu uku (3,000) daga Isra'ila, dubu biyu (2,000) su zauna tare da shi a Mikmash da ƙasar tuddai ta Betel, dubu ɗaya (1,000) kuma su zauna tare da Jonatan a Gibeya ta Biliyaminu, sauran jama'a kuwa ya sallame su, su koma gida, kowa zuwa alfarwarsa.

3. Jonatan kuwa ya kashe wani shugaban yaƙi na Filistiyawa a Geba, Filistiyawa kuwa suka ji labarin abin da ya faru. Sai Saul ya sa aka busa ƙaho ko'ina a ƙasar, na kiran Ibraniyawa su zo yaƙi.

4. Isra'ilawa duka kuwa suka ji wai Saul ya kashe shugaban yaƙi na Filistiyawa, da kuma, Isra'ilawa sun zama abin ƙi ga Filistiyawa, sai jama'a suka amsa kiran, suka tafi wurin Saul a Gilgal.

5. Sai Filistiyawa suka taru don su yi yaƙi da Isra'ilawa. Suka fito da karusa dubu talatin (30,000), da mahayan dawakai dubu shida (6,000), da sojoji da yawa kamar yashi a bakin teku, suka kafa sansani a Mikmash, a wajen gabashin Bet-awen.

6. Sa'ad da Isra'ilawa suka ga sun ƙuntata, gama an matsa su ƙwarai, sai suka ɓuya cikin kogwanni, da cikin ruƙaƙe, da duwatsu, da ramummuka, da kwazazzabai.

Karanta cikakken babi 1 Sam 13