Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 10:10-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Sa'ad da suka iso Gileyad, sai suka tarar da ƙungiyar annabawa. Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko a kansa da iko, sai ya shiga rawa da sowa tare da su.

11. Sa'ad da dukan waɗanda suka san shi, suka gan shi yana yin wannan tare da annabawa, suka ce wa junansu, “Me ya faru da ɗan Kish? Saul kuma yana cikin annabawa ne?”

12. Sai wani mutumin da yake wurin ya ce, “Sauran fa, su ma, iyayensu annabawa ne?” Wannan kuwa ya zama karin magana, “Har Saul kuma yana cikin annabawa?”

13. Da ya gama rawa da sowa sai ya tafi wurin bagaden a kan tudu.

14. Kawun Saul kuwa ya tambaye shi, shi da baransa, “Ina ne kuka tafi?”Saul ya ce, “Mun je neman jakuna, da ba mu same su ba, sai muka tafi wurin Sama'ila.”

15. Kawunsa kuma ya ce, “In ka yarda ka faɗa mini abin da Sama'ila ya faɗa maka.”

16. Saul kuwa ya ce wa kawunsa, “Ya faɗa mana a fili an gane jakunan.” Amma bai faɗa wa kawunsa zancen sarautar da Sama'ila ya faɗa masa ba.

17. Sama'ila kuwa ya tara mutanen Isra'ila a gaban Ubangiji a Mizfa.

18. Ya ce musu, “In ji Ubangiji Allah na Isra'ila, ‘Ni na fito da Isra'ilawa daga Masar, na cece ku daga Masarawa da kuma daga hannun mulkokin da suka wahalshe ku.

19. Ni ne Allahnku wanda yake cetonku daga dukan masifu da wahalai, amma ga shi yau, kun ƙi ni kuna roƙona in ba ku sarki. To, da kyau, yanzu fa sai ku kusato gaban Ubangiji kabila kabila da iyali iyali.’ ”

20. Sa'an nan Sama'ila ya ce wa kabilan Isra'ila su guso, kuri'a kuwa ta faɗa a kan kabilar Biliyaminu.

Karanta cikakken babi 1 Sam 10