Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

1 Sam 1:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Akwai wani mutum daga kabilar Ifraimu sunansa Elkana, yana zaune a Rama, a ƙasar tudu ta Ifraimu. Shi ɗan Yeroham ne, jika ga Eliyab, na iyalin Nahat, daga zuriyar Zuf.

2. Yana da mata biyu, sunayensu Hannatu da Feninna. Feninna tana da 'ya'ya, amma Hannatu ba ta haihuwa.

3. A kowace shekara Elkana yakan haura daga garinsu zuwa Shilo domin ya miƙa wa Ubangiji Mai Runduna hadaya, ya kuma yi masa sujada. 'Ya'yan Eli, maza biyu, Hofni da Finehas, su ne firistoci na Ubangiji a can.

4. Duk lokacin da Elkana ya miƙa hadayarsa, sai ya ba Feninna da 'ya'yanta mata da maza nasu rabo.

5. Amma Hannatu, sai ya ba ta babban rabo guda ɗaya, gama yana ƙaunarta, amma Ubangiji ya kulle mahaifarta.

6. Kishiyarta takan tsokane ta don ta ji haushi, gama Ubangiji ya hana mata haihuwa.

Karanta cikakken babi 1 Sam 1