Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yak 5:9-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. 'Yan'uwa, kada ku yi wa juna gunaguni, don kada a hukunta ku. Ga mai shari'a a bakin ƙofa!

10. A kan misalin shan wuya da haƙuri kuma, 'yan'uwa, ku dubi annabawa ma da suka yi magana da sunan Ubangiji.

11. Ga shi, mukan yaba wa waɗanda suka jure. Kun dai ji irin jimirin da Ayuba ya yi, kun kuma ga irin ƙarshen da Ubangiji ya yi masa, yadda Ubangiji yake mai yawan tausayi, mai jinƙai kuma.

12. Amma fiye da kome, 'yan'uwana, kada ku rantse sam, ko da sama, ko da ƙasa, ko da kowace irin rantsuwa ma. Sai dai in kun ce “I”, ya tsaya a kan “I” ɗin kawai, in kuwa kun ce “A'a”, ya tsaya a kan “A'a” ɗin kawai, don kada a hukunta ku.

13. In waninku yana shan wuya, to, sai ya yi addu'a, in kuma waninku yana murna, to, sai ya yi waƙar yabon Allah.

14. In waninku yana rashin lafiya, to, sai ya kira dattawan ikkilisiya su yi masa addu'a, suna shafa masa mai da sunan Ubangiji.

Karanta cikakken babi Yak 5