Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 8:8-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Sai ya sāke sunkuyawa, ya yi ta rubutu a ƙasa.

9. Su kuwa da suka ji haka suka fita da ɗaya ɗaya, tun daga babbansu har ya zuwa ƙaraminsu, aka bar Yesu shi kaɗai, da matar tsaye a tsakiya.

10. Sai Yesu ya ɗaga, ya ce mata, “Uwargida, ina suke? Ba wanda ya hukunta ki?”

11. Ta ce, “Babu, ya Ubangiji.” Sai Yesu ya ce, “Ni ma ban hukunta ki ba. Yi tafiyarki. Daga yau kada ki ƙara yin zunubi.”]

12. Sai Yesu ya ƙara musu da cewa, “Ni ne Hasken duniya. Wanda yake bi na ba zai yi tafiya a duhu ba, amma zai sami hasken rai,”

13. Saboda haka Farisiyawa suka ce masa, “Kanka kake wa shaida, shaidarka kuwa ba tabbatacciya ba ce.”

14. Yesu ya amsa musu ya ce, “Ko na shaidi kaina, ai, shaidata tabbatacciya ce, domin na san inda na fito, da kuma inda za ni. Amma ku ba ku san inda na fito ba, ko kuma inda za ni.

15. Ku kuna hukunci irin na duniya ne, ni kuwa ba na hukunta kowa.

16. Amma ko da zan yi hukunci, hukuncina na gaskiya ne, domin ba ni kaɗai nake ba, ni da Uba wanda ya aiko ni ne.

17. A Attaurarku ma a rubuce yake, cewa shaidar mutum biyu tabbatacciya ce.

18. Ni ne nake shaidar kaina, Uba da ya aiko ni kuma yana shaidata.”

19. Saboda haka suka ce masa, “Ina Uban naka yake?” Yesu ya amsa ya ce, “Ko ni ko Ubana, ba wanda kuka sani. Da kun san ni, da kun san Ubana ma.”

Karanta cikakken babi Yah 8