Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 8:45-59 Littafi Mai Tsarki (HAU)

45. Amma domin ina faɗar gaskiya, ba kwa gaskata ni.

46. A cikinku wa zai iya haƙƙaƙewa na taɓa yin zunubi? In kuwa gaskiya nake faɗa, to, don me ba kwa gaskata ni?

47. Na Allah yakan saurari Maganar Allah. Abin da ya sa ba kwa sauraronta ke nan, don ku ba na Allah ba ne.”

48. Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Ashe, gaskiyarmu da muka ce kai Basamariye ne, kana kuma da iska.”

49. Yesu ya amsa ya ce, “Ni ba mai iska ba ne. Ubana nake girmamawa, ku kuwa wulakanta ni kuke yi.

50. Ba ni nake nemar wa kaina girma ba, akwai mai nemar mini, shi ne kuma mai yin shari'a.

51. Lalle hakika, ina gaya muku, kowa ya kiyaye maganata ba zai mutu ba har abada.”

52. Sai Yahudawa suka ce masa, “To, yanzu kam, mun tabbata kana da iska. Ai, Ibrahim ya mutu, haka ma annabawa, kana kuwa cewa kowa ya kiyaye maganarka ba zai mutu ba har abada.

53. Wato ka fi ubanmu Ibrahim ne, ya kuwa mutu? Annabawa ma sun mutu! Wa ka mai da kanka ne?”

54. Yesu ya amsa ya ce, “In ma na ɗaukaka kaina, ɗaukakata ba a bakin kome take ba. Ubana shi ne mai ɗaukaka ni, wanda kuke cewa, shi ne Allahnku.

55. Ku ba ku san shi ba, amma ni na san shi. Da na ce ban san shi ba, da na zama maƙaryaci kamarku. Amma na san shi, ina kuma kiyaye magana tasa.

56. Ubanku Ibrahim ya yi farin ciki matuƙa ya sami ganin zamanina, ya kuwa gan shi, ya yi murna.”

57. Sai Yahudawa suka ce masa, “Har yanzu ma ba ka kai shekara hamsin ba, wai kuwa har ka ga Ibrahim!”

58. Sai Yesu ya ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, tun ba a haifi Ibrahim ba, ni ne.”

59. Don haka suka ɗebo duwatsu su jajjefe shi. Yesu kuwa ya ɓuya, ya fita daga Haikalin.

Karanta cikakken babi Yah 8