Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 21:21-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Da Bitrus ya gan shi, ya ce wa Yesu, “Ya Ubangiji, wannan fa?”

22. Yesu ya ce masa, “In na nufe shi da wanzuwa har in zo, mene ne naka a ciki? Kai dai, bi ni!”

23. Saboda haka maganan nan ta bazu cikin 'yan'uwa, cewa almajirin nan ba zai mutu ba. Alhali kuwa Yesu bai ce masa ba zai mutu ba, ya dai ce, “In na nufe shi da wanzuwa har in zo, mene ne naka a ciki?”

24. Wannan shi ne almajirin da yake ba da shaida a kan waÉ—annan al'amura, ya kuma rubuta su, mun kuwa sani shaida tasa tabbatacciya ce.

Karanta cikakken babi Yah 21