Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 21:19-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. (Ya faɗi wannan ne yana kwatanta irin mutuwar da Bitrus zai yi ya ɗaukaka Allah.) Bayan ya faɗi haka, ya ce masa, “Bi ni.”

20. Sai Bitrus ya waiwaya ya ga almajirin nan da Yesu yake ƙauna yana biye da su, wato wanda ya jingina gab da Yesu lokacin cin jibin nan da ya ce, “Ya Ubangiji, wane ne zai bāshe ka?”

21. Da Bitrus ya gan shi, ya ce wa Yesu, “Ya Ubangiji, wannan fa?”

22. Yesu ya ce masa, “In na nufe shi da wanzuwa har in zo, mene ne naka a ciki? Kai dai, bi ni!”

23. Saboda haka maganan nan ta bazu cikin 'yan'uwa, cewa almajirin nan ba zai mutu ba. Alhali kuwa Yesu bai ce masa ba zai mutu ba, ya dai ce, “In na nufe shi da wanzuwa har in zo, mene ne naka a ciki?”

24. Wannan shi ne almajirin da yake ba da shaida a kan waɗannan al'amura, ya kuma rubuta su, mun kuwa sani shaida tasa tabbatacciya ce.

25. Akwai waɗansu al'amura kuma masu yawa da Yesu ya aikata, in da za a rubuta kowannensu ɗaya ɗaya da ɗaya ɗaya, ina tsammani ko duniya kanta ba za ta iya ɗaukar littattafan da za a rubuta ba.

Karanta cikakken babi Yah 21