Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 19:7-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Ai, muna da Shari'a, bisa ga Sharian nan kuwa ya wajaba a kashe shi, saboda ya mai da kansa Ɗan Allah.”

8. Da Bilatus ya ji maganan nan sai ya ƙara tsorata.

9. Ya sāke shiga fāda, ya ce wa Yesu, “Daga ina kake?” Amma Yesu bai amsa masa ba.

10. Saboda haka Bilatus ya ce masa, “Ba za ka yi mini magana ba? Ba ka sani ba ni ne da ikon sakinka, ko gicciye ka?”

11. Yesu ya amsa masa ya ce, “Ba ka da wani iko a kaina in ba an ba ka daga Sama ba, saboda haka wanda ya bāshe ni gare ka ya fi ka zunubi.”

12. A kan wannan Bilatus ya nemi ya sake shi, sai dai Yahudawa suka ɗau kururuwa suna cewa, “In dai ka saki wannan, kai ba masoyin Kaisar ba ne. Ai, kowa ya mai da kansa sarki, ya tayar wa Kaisar ke nan.”

13. Da Bilatus ya ji wannan magana, sai ya fito da Yesu, ya zauna a kan gadon shari'a, wurin da ake kira Daɓe, da Yahudanci kuwa, Gabbata.

14. Ran nan kuwa ranar shirin Idin Ƙetarewa ce, wajen tsakiyar rana. Sai ya ce wa Yahudawa, “Ga sarkinku!”

15. Sai suka ɗau kururuwa suna cewa, “A yi da shi! A yi da shi! A gicciye shi!” Bilatus ya ce musu, “A! In gicciye sarkinku?” Sai manyan firistoci suka amsa suka ce, “Mu ba mu da sarki sai Kaisar.”

16. Sa'an nan ya bāshe shi gare su su gicciye shi.

17. Sai suka tafi da Yesu. Ya kuwa fita, shi kansa yake ɗauke da gicciyensa, har zuwa wurin da ake kira Wurin Ƙoƙon Kai, da Yahudanci kuwa, Golgota.

18. Nan suka gicciye shi, da kuma waɗansu mutum biyu tare da shi, ɗaya ta kowane gefe, Yesu kuwa a tsakiya.

19. Bilatus kuma ya rubuta wata sanarwa, ya kafa ta a kan gicciyen. Abin da aka rubuta ke nan, “Yesu Banazare Sarkin Yahudawa.”

Karanta cikakken babi Yah 19