Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 19:13-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Da Bilatus ya ji wannan magana, sai ya fito da Yesu, ya zauna a kan gadon shari'a, wurin da ake kira Daɓe, da Yahudanci kuwa, Gabbata.

14. Ran nan kuwa ranar shirin Idin Ƙetarewa ce, wajen tsakiyar rana. Sai ya ce wa Yahudawa, “Ga sarkinku!”

15. Sai suka ɗau kururuwa suna cewa, “A yi da shi! A yi da shi! A gicciye shi!” Bilatus ya ce musu, “A! In gicciye sarkinku?” Sai manyan firistoci suka amsa suka ce, “Mu ba mu da sarki sai Kaisar.”

16. Sa'an nan ya bāshe shi gare su su gicciye shi.

17. Sai suka tafi da Yesu. Ya kuwa fita, shi kansa yake ɗauke da gicciyensa, har zuwa wurin da ake kira Wurin Ƙoƙon Kai, da Yahudanci kuwa, Golgota.

18. Nan suka gicciye shi, da kuma waɗansu mutum biyu tare da shi, ɗaya ta kowane gefe, Yesu kuwa a tsakiya.

19. Bilatus kuma ya rubuta wata sanarwa, ya kafa ta a kan gicciyen. Abin da aka rubuta ke nan, “Yesu Banazare Sarkin Yahudawa.”

20. Yahudawa da yawa kuwa sun karanta wannan sanarwa, domin wurin da aka gicciye Yesu kusa da birni ne. An kuwa rubuta ta da Yahudanci, da Romanci, da kuma Helenanci.

Karanta cikakken babi Yah 19