Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 18:30-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. Sai suka amsa masa suka ce, “Da wannan ba mai laifi ba ne, ai, da ba mu bāshe shi gare ka ba.”

31. Bilatus ya ce musu, “Ku tafi da shi da kanku mana, ku hukunta shi bisa ga shari'arku!” Sai Yahudawa suka ce masa, “Ai, ba mu da ikon zartar da hukuncin kisa a kan kowa.”

32. Wannan kuwa don a cika maganar da Yesu ya yi ne, wadda ta kwatanta irin mutuwar da zai yi.

33. Sai Bilatus ya koma cikin fāda, ya kira Yesu ya ce masa, “Ashe, kai ɗin nan, kai ne Sarkin Yahudawa?”

34. Yesu ya amsa ya ce, “Wato wannan faɗarka ce, ko kuwa waɗansu ne suka ce da ni haka a wurinka?”

35. Bilatus ya amsa ya ce, “Ni Bayahude ne? Ai, jama'arku da manyan firistoci su ne suka bāshe ka gare ni. Me ka yi?”

36. Yesu ya amsa ya ce, “Mulkina ba na duniyan nan ba ne. Da mulkina na duniyan nan ne da barorina za su yi yaƙi kada a bāshe ni ga Yahudawa. Amma hakika, mulkina ba daga nan yake ba.”

37. Sai Bilatus ya ce masa, “Wato ashe, sarki ne kai?” Yesu ya amsa ya ce, “Yadda ka faɗa, ni sarki ne. Domin haka musamman aka haife ni, don haka kuma musamman na shigo duniya, domin in shaidi gaskiya. Kowane mai ƙaunar gaskiya kuwa yakan saurari muryata.”

Karanta cikakken babi Yah 18