Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 15:8-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Yadda ake ɗaukaka Ubana ke nan, in kuna 'ya'ya da yawa, ta haka kuma kuke tabbata almajiraina.

9. Kamar yadda Uba ya ƙaunace ni, haka ni ma na ƙaunace ku. To, ku zauna cikin ƙaunar da nake muku.

10. In kun bi umarnina, za ku zauna cikin ƙaunar da nake muku, kamar yadda ni na bi umarnin Ubana, na kuma zauna cikin ƙaunar da yake mini.

11. Na gaya muku haka domin farin cikina ya kasance a cikinku, farin cikinku kuma ya zama cikakke.

12. “Wannan fa shi ne umarnina, cewa ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku.

13. Ba ƙaunar da ta fi haka ga mutane, wato mutum yă ba da ransa saboda aminansa.

Karanta cikakken babi Yah 15