Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 12:29-43 Littafi Mai Tsarki (HAU)

29. Da taron da yake tsaye a wurin suka ji muryar, suka ce, “An yi cida.” Waɗansu kuwa suka ce, “Wani mala'ika ne ya yi masa magana.”

30. Yesu ya amsa ya ce, “Ba saboda ni aka yi wannan muryan nan ba, sai dominku.

31. Yanzu ne za a yi wa duniyan nan shari'a, yanzu ne kuma za a tuɓe mai mulkin duniyan nan.

32. Ni kuwa bayan an ɗaga ni daga ƙasa zan ja dukan mutane gare ni.”

33. Ta faɗar haka ya kwatanta irin mutuwar da zai yi.

34. Sai taron suka amsa masa suka ce, “Shari'armu ta gaya mana, cewa Almasihu zai tabbata har abada. To, yaya za ka ce lalle ne a ɗaga Ɗan Mutum? Wane ne Ɗan Mutum ɗin?”

35. Yesu ya ce musu, “Haske na tare da ku har ɗan lokaci kaɗan na gaba. Ku yi tafiya tun haske na tare da ku, kada duhu ya ci muku. Mai tafiya a cikin duhu bai san inda yake tafiya ba.

36. Ku gaskata da hasken, tun kuna tare da shi, domin ku zama mutanen haske.”Yesu ya faɗi haka, sa'an nan ya tafi ya ɓuya musu.

37. Amma ko da yake ya sha yin mu'ujizai da yawa a gabansu, duk da haka, ba su gaskata shi ba,

38. domin a cika faɗar Annabi Ishaya cewa,“Ya Ubangiji, wa ya gaskata jawabinmu?Ga wa kuma aka bayyana ikon Ubangiji?”

39. Shi ya sa ba su iya ba da gaskiya ba. Domin Ishaya ya sāke cewa,

40. “Ya makantar da su, ya kuma taurarar da zuciya tasu,Kada su gani da idanunsu, su kuma gane a zuci,Har su juyo gare ni in warkar da su.”

41. Ishaya ya faɗi haka saboda ya ga ɗaukakar Almasihu, ya kuma ba da labarinsa.

42. Duk da haka, da yawa har daga cikin shugabanni ma suka gaskata da shi, amma saboda tsoron Farisiyawa, ba su bayyana ba, don kada a fisshe su daga jama'a.

43. Don sun fi ƙaunar girmamawar mutane da girmamawar Allah.

Karanta cikakken babi Yah 12