Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 1:6-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Akwai wani mutum da Allah ya aiko, mai suna Yahaya.

7. Shi fa ya zo shaida ne, domin ya shaidi hasken, kowa yă ba da gaskiya ta hanyarsa.

8. Ba shi ne hasken ba, ya zo ne domin ya shaidi hasken.

9. Akwai hakikanin haske mai shigowa duniya da yake haskaka kowane mutum.

10. Dā yana duniya, duniyar ta wurinsa ta kasance, duk da haka duniya ba ta san shi ba.

11. Ya zo ga abin mulkinsa ne, jama'a tasa kuwa ba ta karɓe shi ba.

12. Amma duk iyakar waɗanda suka karɓe shi, wato, masu gaskatawa da sunansa, ya ba su ikon zama 'ya'yan Allah,

13. wato, waɗanda aka haifa ba daga jini ba, ba daga nufin jiki ko nufin mutum ba, amma daga wurin Allah.

14. Kalman nan kuwa ya zama mutum, ya zauna a cikinmu, yana mai matuƙar alheri da gaskiya. Mun kuma dubi ɗaukakarsa, ɗaukaka ce ta makaɗaicin Ɗa daga wurin Ubansa.

15. Yahaya ya shaida shi, ya ɗaga murya ya ce, “Wannan shi ne wanda na ce, ‘Mai zuwa bayana ya zama shugabana, domin dā ma yana nan tun ba ni.’ ”

16. Dukanmu kuwa daga falala tasa muka samu, alheri kan alheri.

17. Domin Shari'a, ta hannun Musa aka ba da ita, alheri da gaskiya kuwa ta wurin Yesu Almasihu suka kasance.

18. Ba mutumin da ya taɓa ganin Allah daɗai. Makaɗaicin Ɗa, wanda yake yadda Allah yake, wanda kuma yake a wurin Uba, shi ne ya bayyana shi.

19. Wannan kuwa ita ce shaidar Yahaya, wato, sa'ad da Yahudawa suka aiki firistoci da Lawiyawa daga Urushalima su tambaye shi, ko shi wane ne.

Karanta cikakken babi Yah 1