Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 1:27-44 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. shi ne mai zuwa bayana, wanda ko maɓallin takalminsa ma, ban isa in ɓalle ba.”

28. An yi wannan a Betanya ne, a hayin Kogin Urdun, inda Yahaya yake yin baftisma.

29. Kashegari Yahaya ya tsinkayo Yesu na nufo shi, sai ya ce, “Kun ga, ga Ɗan Rago na Allah, wanda zai ɗauke zunubin duniya!

30. Wannan shi ne wanda na ce, ‘Wani yana zuwa bayana, wanda ya zama shugabana, domin dā ma yana nan tun ba ni.’

31. Dā kam, ban san shi ba, sai domin a bayyana shi ga Isra'ila na zo, nake baftisma da ruwa.”

32. Yahaya ya yi shaida ya ce, “Na ga Ruhu na saukowa kamar kurciya daga sama, ya kuma zauna a kansa.

33. Dā kam, ban san shi ba, sai dai wanda ya aiko ni in yi baftisma da ruwa, shi ne ya ce mini, ‘Wanda ka ga Ruhun na sauko masa, yana kuma kasance a kansa, shi ne mai yin baftisma da Ruhu Mai Tsarki.’

34. Na kuwa gani, na kuma yi shaida, cewa wannan Ɗan Allah ne.”

35. Kashegari kuma Yahaya na tsaye da almajiransa biyu.

36. Yana duban Yesu na tafiya, sai ya ce, “Kun ga, ga Ɗan Rago na Allah!”

37. Almajiran nan biyu suka ji ya faɗi haka, sai suka bi Yesu.

38. Yesu ya waiwaya ya ga suna biye da shi, sai ya ce musu, “Me kuke nema?” Suka ce masa, “Ya Rabbi, wato Malam ke nan, ina kake da zama?”

39. Sai ya ce musu, “Ku zo ku gani.” Sai suka je suka ga inda yake da zama, suka kuwa yini tare da shi. Wajen ƙarfe huɗu na yamma ne kuwa.

40. Ɗaya daga cikin biyun nan da suka ji maganar Yahaya suka kuma bi Yesu, Andarawas ne, ɗan'uwan Bitrus.

41. Sai ya fara samo ɗan'uwansa Bitrus, ya ce masa, “Mun sami Almasihu,” wato shafaffe.

42. Sai ya kai shi wurin Yesu. Yesu ya dube shi, ya ce, “Wato kai ne Saminu ɗan Yahaya? Za a kira ka Kefas,” wato Bitrus.

43. Kashegari Yesu ya yi niyyar zuwa ƙasar Galili. Sai ya sami Filibus, ya ce masa, “Bi ni.”

44. Filibus kuwa mutumin Betsaida ne, garin su Andarawas da Bitrus.

Karanta cikakken babi Yah 1