Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. Yah 9:15-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Sai aka saki mala'ikun nan huɗu, waɗanda aka tanada saboda wannan sa'a, da wannan rana, da wannan wata, da wannan shekara, su kashe sulusin 'yan adam.

16. Yawan rundunonin sojan doki kuwa, na ji adadinsu zambar dubu metan ne.

17. Ga kuwa yadda na ga dawakan a wahayin da aka yi mini, mahayansu suna saye da sulkuna, launinsu ja kamar wuta, da shuɗi, da kuma rawaya kamar farar wuta, kawunan dawakan kuma kamar na zaki, wuta kuma da hayaƙi da farar wuta suna fita daga bakinsu.

18. Da waɗannan bala'i uku aka kashe sulusin 'yan adam, wato, da wuta, da hayaƙi, da farar wuta da suke fita daga bakinsu.

19. Domin ikon dawakan nan na a bakinsu da a wutsiyarsu, wutsiyoyinsu kamar macizai suke, har da kawuna, da su ne suke azabtarwa.

20. Sauran 'yan adam waɗanda bala'in nan bai kashe ba kuwa, ba su tuba sun rabu da abubuwan da suka yi da hannunsu ba, ba su kuma daina yin sujada ga aljannu, da gumakan zinariya, da na azurfa, da na tagulla, da na dutse, da na itace ba, waɗanda ba su iya gani, ko ji, ko tafiya,

21. ba su kuma tuba da kashe-kashenkai da suka yi ba, ko sihirinsu, ko fasikancinsu, ko kuma sace-sacensu.

Karanta cikakken babi W. Yah 9