Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. Yah 4:7-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Rayayyiyar halittar farko kamar zaki take, ta biyu kuma kamar ɗan maraƙi, ta uku kuma da fuska kamar ta mutum, ta huɗu kuma kamar juhurma yana jewa.

8. Su rayayyun halittan nan huɗu kuwa, kowaccensu tana da fikafikai shida, jikinsu duk idanu ne ciki da waje, dare da rana kuwa ba sa daina waƙa, suna cewa,“Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki, Ubangiji Allah Maɗaukaki,Shi ne a dā, shi ne a yanzu, shi ne kuma a nan gaba!”

9. Duk lokaci kuma da rayayyun halittan nan suka ɗaukaka wanda yake zaune a kan kursiyin, yake kuma raye har abada abadin, suka girmama shi, suka kuma gode masa,

10. sai dattawan nan ashirin da huɗu suka fāɗi a gaban wanda yake a zaune a kan kursiyin, su yi masa sujada, shi da yake a raye har abada abadin, su kuma ajiye kambinsu a gaban kursiyin, suna waƙa, suna cewa,

11. “Macancanci ne kai, ya Ubangiji Allahnmu,Kă sami ɗaukaka, da girma, da iko,Domin kai ne ka halicci dukkan abubuwa,Da nufinka ne suka kasance aka kuma halicce su.”

Karanta cikakken babi W. Yah 4