Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. Yah 21:5-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Sai na zaune a kan kursiyin ya ce, “Kun ga, ina yin kome sabo.” Ya kuma ce, “Rubuta wannan, domin maganar nan tabbatacciya ce, gaskiya ce kuma.”

6. Sai ya ce mini, “An gama! Ni ne Alfa, Ni ne Omega, Ni ne na Farko, Ni ne kuma na Ƙarshe. Duk mai jin ƙishirwa zan ba shi ruwa daga maɓuɓɓugar ruwan rai kyauta.

7. Duk wanda ya ci nasara, zai ci wannan gādo, wato, in zama Allahnsa, shi kuma ya zama ɗa a gare ni.

8. Amma matsorata, da marasa riƙon amana, da masu aikin ƙyama, da masu kisankai, da fasikai, da masu sihiri, da masu bautar gumaka, da kuma duk maƙaryata, duk rabonsu tafkin nan ne mai cin wuta da kibiritu, wanda yake shi ne mutuwa ta biyu.”

9. Sai kuma ɗaya daga cikin mala'ikun nan bakwai, masu tasoshin nan bakwai, cike da bala'i bakwai na ƙarshe, ya zo ya yi mini magana, ya ce, “Zo in nuna maka amarya, matar Ɗan Ragon.”

10. Sai ya ɗauke ni, Ruhu yana iza ni, ya kai ni wani babban dutse mai tsawo, ya nuna mini tsattsarkan birnin Urushalima yana saukowa daga Sama daga wurin Allah,

11. yana tare da ɗaukakar Allah. Hasken birnin yana ƙyalƙyali kamar wani irin nadirin dutse mai daraja, kamar yasfa, garau kamar ƙarau.

12. Yana da babban garu mai tsawo, da ƙofar gari goma sha biyu, a ƙofofi ɗin da akwai mala'iku goma sha biyu. A jikin ƙofofin kuma an rubuta sunayen kabilan nan goma sha biyu na Isra'ila,

13. a gabas, ƙofa uku, a yamma ƙofa uku, a kudu ƙofa uku, a arewa kuma ƙofa uku.

14. Garun birnin kuwa, tana da dutsen harsashi goma sha biyu, a jikinsu kuma an rubuta sunayen manzannin nan goma sha biyu na Ɗan Ragon.

15. Shi wanda ya yi mini magana kuwa yana da sandar awo ta zinariya, domin ya auna birnin, da ƙofofinsa, da garunsa.

16. Birnin murabba'i ne, tsawonsa da fāɗinsa duka ɗaya ne. Sai ya auna birnin da sandarsa, mil dubu da ɗari biyar, tsawonsa, da fāɗinsa da zacinsa, duka ɗaya suke.

17. Ya kuma auna garunsa, kamu ɗari da arba'in da huɗu ne na mutum, wato, na mala'ika ke nan.

18. Garun kuwa da yasfa aka gina shi, birnin kuma da zinariya zalla, garau kamar ƙarau.

19. An kuma ƙawata harsasan garun birnin da kowane irin dutse mai daraja. Yasfa shi ne na farko, na biyu saffir, na uku agat, na huɗu zumurrudu,

20. na biyar onis, na shida yaƙutu, na bakwai kirisolat, na takwas beril, na tara tofaz, na goma kirisofaras, na sha ɗaya yakinta, na sha biyu kuma ametis.

21. Ƙofofin gari goma sha biyun nan kuwa lu'ulu'u ne goma sha biyun, kowace ƙofa da lu'ulu'u guda aka yi ta, hanyar birnin kuwa zinariya ce zalla garau kamar ƙarau.

22. Ban kuwa ga wani Haikali a birnin ba, domin Haikalinsa Ubangiji Allah Maɗaukaki ne, da kuma Ɗan Ragon.

Karanta cikakken babi W. Yah 21