Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. Yah 21:5-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Sai na zaune a kan kursiyin ya ce, “Kun ga, ina yin kome sabo.” Ya kuma ce, “Rubuta wannan, domin maganar nan tabbatacciya ce, gaskiya ce kuma.”

6. Sai ya ce mini, “An gama! Ni ne Alfa, Ni ne Omega, Ni ne na Farko, Ni ne kuma na Ƙarshe. Duk mai jin ƙishirwa zan ba shi ruwa daga maɓuɓɓugar ruwan rai kyauta.

7. Duk wanda ya ci nasara, zai ci wannan gādo, wato, in zama Allahnsa, shi kuma ya zama ɗa a gare ni.

8. Amma matsorata, da marasa riƙon amana, da masu aikin ƙyama, da masu kisankai, da fasikai, da masu sihiri, da masu bautar gumaka, da kuma duk maƙaryata, duk rabonsu tafkin nan ne mai cin wuta da kibiritu, wanda yake shi ne mutuwa ta biyu.”

9. Sai kuma ɗaya daga cikin mala'ikun nan bakwai, masu tasoshin nan bakwai, cike da bala'i bakwai na ƙarshe, ya zo ya yi mini magana, ya ce, “Zo in nuna maka amarya, matar Ɗan Ragon.”

10. Sai ya ɗauke ni, Ruhu yana iza ni, ya kai ni wani babban dutse mai tsawo, ya nuna mini tsattsarkan birnin Urushalima yana saukowa daga Sama daga wurin Allah,

11. yana tare da ɗaukakar Allah. Hasken birnin yana ƙyalƙyali kamar wani irin nadirin dutse mai daraja, kamar yasfa, garau kamar ƙarau.

12. Yana da babban garu mai tsawo, da ƙofar gari goma sha biyu, a ƙofofi ɗin da akwai mala'iku goma sha biyu. A jikin ƙofofin kuma an rubuta sunayen kabilan nan goma sha biyu na Isra'ila,

Karanta cikakken babi W. Yah 21