Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. Yah 18:10-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. za su tsaya a can nesa, don tsoron azabarta, su ce,“Kaitonka! Kaitonka, ya kai babban birni!Ya kai birni mai ƙarfi, Babila!A sa'a ɗaya hukuncinka ya auko.”

11. Attajiran duniya kuma suna yi mata kuka suna baƙin ciki, tun da yake, ba mai ƙara sayen kayansu,

12. wato, zinariya, da azurfa, da duwatsun alfarma, da lu'ulu'u, da lallausan lilin, da hajja mai ruwan jar garura, da siliki, da jan alharini, da itacen ƙanshi iri iri, da kayan hauren giwa iri iri, da kayan da aka sassaƙa da itace mai tsada, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na dutse mai sheƙi,

13. da kirfa, da kayan yaji, da turaren wuta, da mur, da lubban, da ruwan inabi, da mai, da garin alkama, da alkama, da shanu, da tumaki, da dawaki, da kekunan doki, da kuma bayi, wato, rayukan 'yan adam.

14. “Amfanin da kika ƙwallafa rai a kai, har ya kuɓuce miki,Kayan annashuwarki da na adonki sun ɓace miki, ba kuwa za a ƙara samunsu ba har abada!”

15. Attajiran waɗannan hajjoji da suka arzuta a game da ita, za su tsaya a can nesa don tsoron azabarta, suna kuka, suna baƙin ciki, suna cewa,

16. “Kaito! Kaiton babban birnin nan!Wanda dā ya sa lallausan lilin, da tufafi masu ruwan jar garura, da kuma jan alharini,Wanda ya ci ado da kayan zinariya, da duwatsun alfarma, da lu'ulu'u!

17. Domin a sa'a ɗaya duk ɗumbun dukiyar nan ta hallaka.”Sai duk masu jiragen ruwa, da masu shiga, da masu tuƙi, da duk waɗanda cinikinsu ya gamu da bahar, suka tsaya a can nesa,

18. suna kururuwa da suka ga hayaƙin ƙunarsa, suna cewa,“Wane birni ne ya yi kama da babban birnin nan?”

19. Har suka tula wa kansu ƙasa suna ta kuka, suna baƙin ciki, suna kururuwa, suna cewa,“Kaito! Kaiton babban birnin nan!Wanda duk masu jiragen ruwa a bahar suka arzuta da ɗumbun dukiyarsa,A sa'a ɗaya ya hallaka.

20. Ki yi farin ciki saboda an yi masa haka, ya sama!Ku yi farin ciki, ku tsarkaka da manzanni da annabawa, domin Allah ya rama muku abin da ya yi muku!”

21. Sai wani ƙaƙƙarfan mala'ika ya ɗauki wani dutse kamar babban dutsen niƙa, ya jefa a teku, ya ce,“Haka za a fyaɗa Babila babban birni, da ƙarfi, ba kuwa za a ƙara ganinta ba.

Karanta cikakken babi W. Yah 18