Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. Yah 10:5-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Sai mala'ikan nan da na gani a tsaye a teku da ƙasa ya ɗaga hannunsa na dama sama,

6. ya rantse da wanda yake a raye har abada abadin, wanda ya halicci sama da abin da take a cikinta, da ƙasa da abin da take a cikinta, da kuma teku da abin da take a cikinta, cewa ba sauran wani jinkiri kuma,

7. sai dai a lokacin busa ƙahon da mala'ika na bakwai zai busa ne, za a cika asirtaccen nufin nan na Allah, bisa ga bisharar da ya yi wa bayinsa annabawa.

8. Sa'an nan muryar nan da na ji daga sama ta sāke yi mini magana, ta ce, “Je ka, ka ɗauki littafin nan da yake a buɗe a hannun mala'ikan da yake a tsaye a bisa teku da ƙasa.”

9. Sai na je wurin mala'ikan, na ce masa, ya ba ni ƙaramin littafin. Sai ya ce mini, “Karɓi ka cinye, zai yi maka ɗaci a ciki, amma a baka kamar zuma yake don zaƙi.”

10. Sai na karɓi ƙaramin littafin daga hannun mala'ikan, na cinye. Sai ya yi zaƙi kamar zuma a bakina, amma da na cinye, cikina ya ɗau ɗaci.

11. Sai kuma aka ce mini, “Lalle ne ka sāke yin annabci a game da jama'a iri iri, da al'ummai, da harsuna, da kuma sarakuna da yawa.”

Karanta cikakken babi W. Yah 10