Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Tit 1:9-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. mai riƙe da tabbatacciyar maganar nan kankan, daidai yadda aka koya masa, domin yă iya ƙarfafa wa waɗansu zuciya da sahihiyar koyarwa, ya kuma ƙaryata waɗanda suka yi musunta.

10. Don kuwa akwai kangararrun mutane da yawa, da masu surutan banza, da masu ruɗi, tun ba ma ɗariƙar masu kaciyar nan ba.

11. Lalle ne a kwaɓe su, tun da yake suna jirkitar da jama'a gida gida, ta wurin koyar da abin da bai kamata ba, don neman ƙazamar riɓa.

12. Wani annabi na Karitawa ya ce, “Karitawa a kullum maƙaryata ne, mugayen dabbobi, ragwaye, haɗamammu.”

13. Shaidar nan tasa kuwa gaskiya ce. Saboda haka, dai ka tsawata musu da gaske, domin su zama sahihai a wajen bangaskiya,

14. a maimakon su mai da hankali ga almarar Yahudawa, ko kuwa dokokin mutane masu ƙin gaskiya.

15. Ga masu tsarkin rai duk al'amarinsu mai tsarki ne, marasa tsarkin rai kuwa marasa ba da gaskiya, ba wani al'amarinsu da yake mai tsarki, da zuciyarsu da lamirinsu duka marasa tsarki ne.

Karanta cikakken babi Tit 1