Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Tit 1:6-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. sai wanda ya kasance marar abin zargi, mai mace ɗaya, wanda 'ya'yansa suke masu ba da gaskiya, waɗanda ba a zarginsu da aikin masha'a ko na kangara.

7. Lalle ne kuwa, kowane mai kula da ikkilisiya, da yake shi mai riƙon amana saboda Allah ne, yă zama marar abin zargi, ba mai taurinkai ba, ko mai saurin fushi, ko mashayi, ko mai saurin dūka, ko mai kwaɗayin ƙazamar riba.

8. Amma yă kasance mai yi wa baƙi alheri, mai son abu nagari, natsattse, mai kirki, tsarkakakke, mai kamunkai,

9. mai riƙe da tabbatacciyar maganar nan kankan, daidai yadda aka koya masa, domin yă iya ƙarfafa wa waɗansu zuciya da sahihiyar koyarwa, ya kuma ƙaryata waɗanda suka yi musunta.

10. Don kuwa akwai kangararrun mutane da yawa, da masu surutan banza, da masu ruɗi, tun ba ma ɗariƙar masu kaciyar nan ba.

11. Lalle ne a kwaɓe su, tun da yake suna jirkitar da jama'a gida gida, ta wurin koyar da abin da bai kamata ba, don neman ƙazamar riɓa.

12. Wani annabi na Karitawa ya ce, “Karitawa a kullum maƙaryata ne, mugayen dabbobi, ragwaye, haɗamammu.”

13. Shaidar nan tasa kuwa gaskiya ce. Saboda haka, dai ka tsawata musu da gaske, domin su zama sahihai a wajen bangaskiya,

Karanta cikakken babi Tit 1