Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rom 9:12-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. aka ce mata, “Wan zai bauta wa ƙanen.”

13. Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yakubu na so, Isuwa na ƙi.”

14. To, me kuma za mu ce? Allah ya yi rashin adalci ke nan? a'a, ko kusa!

15. Domin ya ce wa Musa, “Wanda zan yi wa jinƙai, zan yi masa jinƙan, wanda zan nuna wa tausayi kuwa, zan nuna masa tausayin.”

16. Ashe kuwa, abin bai danganta ga nufin mutum ko himma tasa ba, sai dai ga jinƙan Allah.

17. Don a Nassi an ce da Fir'auna, “Na girmama ka ne musamman, domin in nuna ikona a kanka, domin kuma a sanar da sunana a duniya duka.”

18. Wato, yana nuna jinƙai ga wanda ya so, yana kuma taurara zuciyar wanda ya so.

19. Kila ka ce mini, “To, don me har yanzu yake ganin laifi? Wa zai iya tsayayya da nufinsa?”

20. Ya kai ɗan adam! Wane ne kai har da za ka yi jayayya da Allah? Ashe, abin da aka gina zai iya ce wa magininsa, “Don me ka yi ni haka?”

21. Ashe, maginin tukwane ba ya iko da yumɓu, ya gina wata domin aiki mai martaba, wata kuma don kasasshen aiki, duk daga curi ɗaya?

22. To, ƙaƙa fa? Allah da yake yana so ya nuna fushinsa, ya kuma bayyana ikonsa, sai ya haƙura matuƙar haƙuri da waɗanda suka cancanci fushinsa, suka kuma isa hallaka,

23. Nufinsa ne yă bayyana yalwar ɗaukakarsa ga waɗanda ya yi wa jinƙai, wato, waɗanda dā ma ya yi wa tanadin ɗaukaka?

24. Wato, mu ke nan da ya kira, ba kuwa daga cikin Yahudawa kaɗai ba, har ma daga cikin al'ummai.

25. Kamar dai yadda ya faɗa a Littafin Yusha'u cewa,“Waɗanda dā ba jama'ata ba,Zan ce da su ‘jama'ata,’Wadda dā ba abar ƙaunata ba kuma,Zan ce da ita ‘abar ƙaunata.’ ”

26. “A daidai wurin da aka ce da su, ‘Ku ba jama'ata ba ne,’A nan ne za a kira su ‘'ya'yan Allah Rayayye,’ ”

27. A game da Isra'ila Ishaya ma ya ɗaga murya ya ce, “Ko da yake yawan Isra'ilawa ya kai kamar yashin teku, duk da haka kaɗan ne za su sami ceto.

28. Domin Ubangiji zai zartar da hukuncinsa a duniya, ya gama shi tashi ɗaya.”

Karanta cikakken babi Rom 9