Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rom 8:27-36 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. Amma shi mai fayyace zukatanmu ya san abin da Ruhu yake niyya, domin bisa ga nufin Allah ne Ruhu yake yi wa tsarkaka roƙo.

28. Mun kuma sani al'amura duka suna aikatawa tare, zuwa alheri ga waɗanda suke ƙaunar Allah, wato, waɗanda suke kirayayyu bisa ga nufinsa.

29. Waɗanda Allah ya riga ya zaɓa tun tuni, su ne ya ƙaddara su ɗauki kamannin Ɗansa, domin shi Ɗan yă zama na farko a cikin 'yan'uwa masu yawa.

30. Waɗanda ya ƙaddarar nan kuwa, su ne ya kira. Waɗanda ya kira kuwa, su ne ya kuɓutar. Waɗanda ya kuɓutar ɗin kuwa, su ne ya ɗaukaka.

31. To, me kuma za mu ce a game da haka? Da yake Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu?

32. Shi da bai hana Ɗansa ba, sai ma ya ba da shi saboda mu duka, ashe, ba zai ba mu kome tare da shi hannu sake ba?

33. Wa zai ɗora wa zaɓaɓɓun Allah laifi? Allah ne yake kuɓutar da su!

34. Wa zai hukunta su? Almasihu Yesu wanda ya mutu, ko kuwa a ce wanda ya tashi daga matattu, shi ne wanda yake zaune dama ga Allah, shi ne kuwa wanda yake roƙo saboda mu!

35. Wa zai iya raba mu da ƙaunar da Almasihu yake yi mana? Ƙunci ne? ko masifa? ko tsanani? ko yunwa? ko huntanci? ko hatsari? ko takobi?

36. Kamar yadda yake a rubuce cewa,“Saboda kai ne ake kashe mu yini zubur,An lasafta mu kamar tumakin yanka.”

Karanta cikakken babi Rom 8