Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rom 5:11-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Banda haka ma, har muna fariya da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ta wurinsa ne muka sami sulhun nan a yanzu.

12. To, kamar yadda zunubi ya shigo duniya ta dalilin mutum ɗaya, zunubi kuwa shi ya jawo mutuwa, ta haka mutuwa ta zama gādo ga kowa, don kowa ya yi zunubi.

13. Lalle fa zunubi yana nan a duniya tun ba a ba da Shari'a ba, sai dai inda ba shari'a, ba a lasafta zunubi.

14. Duk da haka kuwa mutuwa ta mallaka tun daga Adamu har ya zuwa Musa, har ma a kan waɗanda ba su yi zunubi irin na keta umarnin da adamu ya yi ba, wanda yake shi ne kwatancin mai zuwan nan.

15. Amma fa baiwar nan dabam take ƙwarai da laifin nan. Ai, in laifin mutum ɗayan nan ya jawo wa masu ɗumbun yawa mutuwa, ashe ma, alherin Allah, da kuma baiwar nan, albarkacin alherin Mutum ɗaya, Yesu Almasihu, sai su yalwata ga masu ɗumbun yawa fin haka ƙwarai.

16. Baiwar nan kuwa dabam take ƙwarai da hakkokin zunubin mutum ɗayan nan. Don kuwa hukuncin da aka yi a kan laifin mutum ɗayan nan, shi ya jawo hukuncin hallaka. Amma baiwar nan da aka yi a sanadin laifofi da yawa, ita take sa kuɓuta ga Allah.

17. In kuwa saboda laifin mutum ɗayan nan ne mutuwa ta yi mallaka ta wurinsa, ashe kuwa, waɗanda suke samun alherin nan mayalwaci, da kuma baiwar nan ta adalcin Allah, sai su yi mallaka fin haka ƙwarai a cikin rai, ta wurin ɗayan nan, wato Yesu Almasihu.

18. To, kamar yadda laifin mutum ɗayan nan ya jawo wa dukan mutane hukunci, haka kuma aikin adalci na Mutum ɗayan nan ya zama wa dukan mutane sanadin kuɓuta zuwa rai.

19. Kamar yadda masu ɗumbun yawa suka zama masu zunubi ta wurin rashin biyayyar mutum ɗaya, haka kuma ta wurin biyayyar Mutum ɗaya za a mai da masu ɗumbun yawa masu adalci.

20. Shari'a fa, an shigo da ita ne, don laifi yă haɓaka. Amma a inda zunubi ya haɓaka, alherin Allah ma ya fi haɓaka ƙwarai da gaske.

21. Wato kamar yadda mallakar zunubi mutuwa ce, haka mallakar Allah ta wurin alheri adalci ce, da take bi da mu zuwa rai madawwami ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu.

Karanta cikakken babi Rom 5