Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rom 4:2-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Gama in da Ibrahim ya sami kuɓuta ta aikinsa na lada, ashe kuwa, yana da abin yin taƙama ke nan, amma fa ba a gaban Allah ba.

3. To, me Nassin ya ce? “Ibrahim ya gaskata Allah, bangaskiyar nan tasa kuma aka lasafta ta adalci ce a gare shi.”

4. Wanda yake aikin lada, ladarsa ba kyauta ba ce, sakamakon aikinsa ce.

5. Wanda ba ya aikin lada, amma yana dogararsa ga Allah, wanda yake kuɓutar da masu laifi, akan lasafta bangaskiyar nan tasa adalci ce.

6. Haka kuma Dawuda ya yi maganar albarkar da aka yi wa mutumin da Allah yake lasafta adalci a gare shi, ba don ya yi aikin lada ba,

7. da ya ce,“Albarka tā tabbata ga waɗanda aka yafe wa laifofinsu,Waɗanda kuma aka shafe zunubansu,

8. Albarka tā tabbata ga wanda faufau Ubangiji ba zai lasafta zunubansa ba.”

9. To, wannan albarka, masu kaciya ne kawai ake yi wa, ko kuwa har da marasa kaciya ma? Gama abin da muke cewa shi ne, “Aka lasafta bangaskiyar Ibrahim adalci ce a gare shi.”

10. To, a cikin wane hali aka lasafta masa ita? Bayan da aka yi masa kaciya ne, ko kuwa tun ba a yi ba? Ai, tun ba a yi ba ne, ba bayan da aka yi ba.

11. Kaciyar da aka yi masa alama ce, wato tabbatacciyar shaida ce ta samun adalci, albarkacin bangaskiyar da yake da ita tun ba a yi masa kaciya ba. Wannan kuwa, domin yă zama uban dukkan masu ba da gaskiya ne, domin su ma a lasafta su masu adalci ne, ba tare da an yi musu kaciya ba,

Karanta cikakken babi Rom 4