Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rom 3:13-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. “Maƙogwaronsu kamar buɗaɗɗen kabari ne,Maganarsu ta yaudara ce.”“Masu ciwon baki ne.”

14. “Yawan zage-zage da ɗacin baki gare su.”

15. “Masu hanzarin zub da jini ne,

16. Ta ko'ina suka bi sai hallaka da baƙin ciki,

17. Ba su kuma san hanyar salama ba.”

18. “Babu tsoron Allah a cikin sha'aninsu sam.”

19. To, mun sani duk abin da Shari'a ta ce, ya shafi waɗanda suke ƙarƙashinta ne, don a tuƙe hanzarin kowa, duk duniya kuma tă sani ƙarƙashin hukuncin Allah take.

20. Ai, ba wani ɗan adam da zai sami kuɓuta ga Allah ta kiyaye ayyukan Shari'a, tun da yake ta Shari'a ne mutum yake ganin laifinsa.

21. A yanzu, ba kuwa a game da shari'a ba, an bayyana wata hanyar samun adalcin Allah, wadda ma Attaura da littattafan annabawa suke yi wa shaida.

22. Adalcin nan na Allah, wanda yake samuwa ta wurin bangaskiya ga Yesu Almasihu, na masu ba da gaskiya ne dukka, ba kuwa wani bambamci,

23. gama 'yan adam duka sun yi zunubi, sun kasa kuma ga ɗaukakar Allah.

24. Amma ta wurin alherin da Allah ya yi musu kyauta, sun sami kuɓuta ta wurin fansar da Almasihu Yesu ya yi.

Karanta cikakken babi Rom 3