Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rom 3:1-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. To, ina fifikon Bayahude? Ko kuma ina fa'idar kaciya?

2. Ai kuwa, akwai ƙwarai, ta kowace hanya. Da farko dai, Yahudawa su ne aka amince wa a game da zantuttukan Allah.

3. To, ƙaƙa ke nan in waɗansu sun ci amanar nan? Sai cin amanarsu ya shafe cikar alkawarin Allah?

4. A'a, ko kusa! A dai tabbata Allah mai gaskiya ne, ko da yake kowane mutum maƙaryaci ne, yadda yake a rubuce cewa,“Don maganarka tă tabbatar da adalcinka,Ka kuma yi rinjaye in an binciki al'amarinka.”

5. In kuwa rashin adalcinmu shi ne yake nuna adalcin Allah a fili, me za mu ce? in Allah ya hore mu, ya yi rashin adalci ke nan? (Misali nake yi kawai.)

6. A'a, ko kusa! To, in da haka ne, ta ƙaƙa Allah zai yi wa duniya shari'a?

7. In kuwa, a dalilin ƙaryata, gaskiyar Allah ta ƙara bayyana, har aka kara ɗaukaka shi, to, don me har yanzu ake hukunta ni a kan ni mai zunubi ne?

8. In haka ne, ba sai mu yi ta yin mugun aiki don ya zama sanadin nagarta ba? Kamar yadda dai waɗansu suke mana yanke, cewa haka muke faɗa. Hukuncin da za a yi wa irin waɗannan kuwa daidai ne.

9. To, ƙaƙa? Mu Yahudawa mun fi sauran ne? A'a, ko kaɗan! Don dā ma mun ɗora wa Yahudawa da al'ummai laifi, cewa dukkansu zunubi yana iko da su.

10. Kamar yadda yake a rubuce cewa,“Babu wani mai adalci, babu, ko ɗaya,

11. Babu wani mai fahimta, babu wani mai neman Allah.

12. Duk sun bauɗe, sun zama marasa amfani baki ɗaya,Babu wani mai aiki nagari, babu kam, ko da guda ɗaya.”

13. “Maƙogwaronsu kamar buɗaɗɗen kabari ne,Maganarsu ta yaudara ce.”“Masu ciwon baki ne.”

14. “Yawan zage-zage da ɗacin baki gare su.”

15. “Masu hanzarin zub da jini ne,

16. Ta ko'ina suka bi sai hallaka da baƙin ciki,

Karanta cikakken babi Rom 3