Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rom 2:4-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Ko kuwa kana raina yalwar alherinsa, da jimirinsa, da kuma haƙurinsa ne? Ashe, ba ka sani ba alherin Allah yana jawo ka zuwa ga tuba?

5. Amma ga shi, saboda ƙeƙasasshiyar zuciyarka marar tuba, kana nema wa kanka fushin Allah a ranar fushi, sa'ad da za a bayyana hukuncin Allah macancani.

6. Allah ne zai saka wa kowa gwargwadon aikinsa.

7. Waɗanda suke neman daraja da ɗaukaka da kuma dawwama ta wurin naciyarsu ga aikata nagarta, zai saka musu da rai madawwami.

8. Waɗanda suke masu sonkai, da waɗanda suke ƙin bin gaskiya, da masu bin rashin adalci, zai saka musu da fushi da hasala.

9. Duk waɗanda suke aikata mugunta za su sha wahala da masifa, da fari Yahudawa, sa'an nan kuma al'ummai.

10. Amma Allah zai ba da daraja, da ɗaukaka, da salama ga dukan waɗanda suke aikata nagarta, da fari ga Yahudawa, sa'an nan ga al'ummai.

11. Domin kuwa, Allah ba ya nuna tara.

12. Ɗaukacin waɗanda suka yi zunubi a rashin sanin Shari'a, za su hallaka ne ba tare da Shari'a ba. Ɗaukacin waɗanda suka yi zunubi a ƙarƙashin Shari'a kuwa, za a hukunta su ta hanyar Shari'a.

13. Don ba ta jin shari'ar kawai mutum yake samun kuɓuta ga Allah ba, sai dai masu aikata ta, su ne za su kuɓuta.

14. In al'ummai, su da ba su da Shari'a, jikinsu ya ba su suka bi umarnin Shari'a, ko da yake ba su da Shari'ar, ashe kuwa, suna da shari'a ke nan.

15. Ayyukansu sun nuna, cewa abin da Shari'a ta umarta a rubuce yake a cikin zukatansu, lamirinsu kuwa yana shaidawa, tunaninsu kuwa yana zarginsu, ko kuma yana kāre su.

Karanta cikakken babi Rom 2